Lokacin da jiragen yakin saman Faransa suka yi barin boma-bomai akan motocin daukar kaya guda arba’in da ake zargin na ‘yan bindiga ne a satin da ya wuce a kasar Chadi, kasar da ta yi wa mulki mallaka, ta nuna a shirye ta ke a fili ta kulla dangantakar sojoji da kasar ta arewacin Afrika
Amma masu lura da al'amura, ciki har dashugabanin ‘yan adawar Chadi, su na tambayar ko shin hare-haren jiragen saman da ta kai an yi nufin a yaki ‘yan ta’adda ne ko anyi ne domin karfafa gwiwar shugaba IDriss Deby wanda ya jagoranci kasar na kusan tsawon shekaru talatin.
Ranar uku ga watan Fabrairu, jiragen yakin saman Faransa su ka kai farmaki a kan jerin gwanon motocin daukar kaya da suke dauke da makamai da suka shiga cikin Chadi daga makwabciyarta Libya. Wanda aka yi kwana hudu ana kai musu hari da jiragen sama.
Faransa ta ce ta amsa neman taimakon da gwamnatin Chadi ta nema ne, ta na mai bayyana Chadi da kasa mai muhimmanci a yaki da ‘yan ta’adda.
Facebook Forum