A maraicen jiya Talata ce ake sa ran shugabannin kasashen Senegal, da Togo, da Benin da kuma Najeriya suka yi balaguro zuwa Ouagadougou domin shawarwari na maida mulki hanun farar hula da sojojin tsaro a fadar shugaban kasa suka ayyana.
Madugun sojojin da suka yi juyin mulkin Janar Gilbert Diendere yace zai mika mulki da zarar kungiyar ECOWAS ta bukaci yayi haka, wadanda shugabannin kasashe da suke cikin kungiyar suka yi taro tunda farko a Abujan Najeriya jiya Talata.
Jakadan Faransa Gilles Thibault ya fada ta shafin Twitter cewa an sako shugaban Burkina na wucin gadi Michael Kafando.
Ahalinda ake ciki kuma, Ma’aikkatar Harkokin Wajen Amurka ta shawarci Amurkawa dake Burkina Faso su bar kasar, saboda wasu dalilan tsaro da basu fayyace ba. Ta kuma shawarci Amurkawa kada suyi balaguro zuwa kasar.
Ana zaman dar dar a birnin Ouagadougou tun bayan da sojojin kasar suka fantsama cikin birnin suka ce suna shirin sarandar sojojin da suka ayyana juyin mulkin.