Shugaban na Chad Idriss Deby yace askarawan rundunar regima masu gadin fadar shugaban kasarBurkina Faso sojoji ne amma kuma su ma ‘ya’yanBurkina Faso ne. A matsayina na dan uwansu ina kira garesu kadda su maida hannun agogon baya a tafiyar wannan kasa kuma ba dai dai ba ne su yi garkuwa da al’umar kasarsu. Su sojoji ne saboda haka abu mafi kyau su ajiye makamai su koma barikinsusu sa ido gwamnatin rikon kwaryar kasar ta ci gaba da shirye shiryen zaben da ake saran gudanarwa a ranar 11 ga watan oktoba mai zuwa.
Jamhuriyar Nijer namakwaftaka da Burkina Faso ta iyakar ta ta bangaren yamma sabilin haka ne shugaban kasa ISUHU MAHAMMAADU ya nuna damuwa akan yiyuwar rikicin na Burkina Faso ya tilastawa wasu ‘yan kasar zuwa hijira cikin kasar Nijer.
ISUHU MAHAMMADU yace muna fata wutar rikicin kasar Burkina Faso ta mutu cikin gaugawa saboda haka muke bukata. A saurari bukatun al’umar Burkina Faso domin a bi ra’ayin talakkawan kasar ita kadai ce mafitar da za ta baiwa kungiyar ECOWAS hanyar warware kiki-kakar da ake fuskanta a wannan kasa.
Shuwabannin biyu Idriss Deby na Chad da Isuhu Mahammadu na Nijer mai masaukin baki sun bayyana cewa matsalar Boko Haram ta kusa kawo karshe ganin yadda kungiyar ta galabaita sakamakon hare haren da take sha a baya bayan nan daga sojojin hadin guiwa.
Ga rahoto.