A cikin watan Afrilun da ya shige, mutane fiye da miliyan 75 aka yi ma rfigakafin cutar shan inna ko Polio a wasu kasashe 22 na Afirka dake cikin wani shiri na Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya. Wasu kasashen su 39 sun karbi magungunan yin rigakafin cutar Polio da wasu cututtukan da ake iya yin rigakafinsu.
Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan gagarumin aikin yin rigakafi lokaci guda a kasashe da dama haka. A bayan cutar ta Polio, an kuma yi allurorin rigakafin wasu cututtukan da dama ciki har da tarin fuka, cutar hanta., bakon dauro, sankarau, cutar hakarkari da dai sauransu.
An kaddamar da wannan shirin da aka sanya ma suna makon Rigakafi na Nahiya a Kinshasa, babban birnin kasar Kwango ta Kinshasa. Firayim ministan kasar, Adolphe Mozito, shi ne ya kaddamar da nufin karfafa ayyukan rigakafi ta hanyar kara wayar da kan jama'a game da muhimmanci da bukata da kuma ikon da jama'a suek da shi na samun kariya daga wadannan cututtukan.
Mr. Muzito yace rigakafi yana bayar da kariya, kuma akwai shi. Saboda haka ya kamata a nemi rigakafin ba tare da jinkiri ba. yayi kira ga 'yan Afirka da su rungumi rigakafin hannu bibbiyu, su kuma tabbatar da cewa an yi rigakafi ma dukkan yara 'yan kasa da shekara biyar da haihuwa.