Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Fama Da Karancin Cibiyoyin Lafiya


Wasu mata su na hutawa bayan da aka yi musu tiyatar magance yoyon fitsari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wasu mata su na hutawa bayan da aka yi musu tiyatar magance yoyon fitsari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A bayan matsalolin karancin cibiyoyin kiwon lafiya, al’adu su na kawo cikas ga yunkurin kula da lafiyar jama’a a wannan kasa da ta fi yawan jama’a a Afirka.

Najeriya ta fi kowace kasa yawan jama’a a nahiyar Afirka. Cibiyoyin kiwon lafiya sun yi kadan sosai a yankunan karkara inda jama’a suka fi yawa, sannan akwai karancin ma’aikata ko na kayan aiki da magunguna a wurare kalilan da ake da cibiyoyin.

A wasu wuraren kuwa, al’adu da halayyan zamantakewa su na takaita zuwan mata domin kula da lafiya a asibitocin.

Najeriya tana da jama’ar da yawansu ya kai kashi 2 cikin 100 ne na al’ummar duniya, amma kashi 10 cikin 100 na dukkan mace-macen mata lokacin haihuwa yana faruwa a kasar.

Kungiyar Engender Health, wadda ta fara aiki a Najeriya a 1985 domin fadada kayyade iyali a kasar, yanzu ta komo ga maida hankali wajen rigakafi tare da jinyar ciwon Yoyon Fitsari. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa mata dubu 800 suek fama da wannan ciwo a Najeriya, kuma kimanin dubu 20 ke kamuwa da shi kowace shekara.

Kungiyar EngenderHealth, mai gudanar da shirin yaki da yoyon fitsari da ake kira “Fistula Care Project” tare da tallafin Hukumar Tallafawa Kasashe Masu Tasowa ta Amurka, watau USAID, tana gudanar da ayyukanta ne a yankin Arewacin Najeriya, inda aka fi fama da mace-macen uwaye, da rashin kayyade iyali, da rashin zuwa awu, da kuma rashin haihuwa a asibiti.

Wannan shirin na yaki da ciwon yoyon fitsari a Najeriya yana aiki da wasu asibitoci guda shida a jihohin Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Kano da Katsina, sai kuma jihar Ebonyi wadda ita ce kadai ba ta arewacin Najeriya.

Ana iya samun karin bayani kan wannan yunkurin a dandalin kungiyar na Internet www.engenderhealth.org

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG