A karon farko hadakar wasu matasa ‘yan kasar Pakistani, sun kirkiri wata kujerar guragu mai sarrafa kanta, matasan da suke daliban wata jami’a a kasar. Sun bayyana wannan a mastayin aiki da ba’a taba gudanar da shi a fadin duniya ba.
Ita dai kujerar ana sarrafa kanta ne da muryar mutun, wanda a duk lokacin da mutane nakasassu ke bukatar taimakon gaggawa, kujerar zata basu duk taimakon da ya kamata batare da sun jira wani ba.
Abu da kawai mutun zai bukata shine, ya gayama kujerar inda yake so tabi, kodai tayi kwana ko ta matsa baya ko gaba, duk abun da mutun ya fada mata zata yi cikin sauri.
Ya zuwa yanzu dai sun samu kamfanoni daga kasar Japan da Germany, suna bukatar su sayar masu da fasahar, dan hakai an fara sayar da kujerar akan kimanin kudi dalar Amurka $800 dai-dai da Naira dubu dari biyu.
Masu bukata zasu iya sayen wannan kujerar daga watan gobe idan Allah ya kai rai. Matasan sun bayana cewar suna da burin habaka wannan fasahar tasu a nan gaba kadan ta wasu hanyoyi daban.
Facebook Forum