WASHINGTON DC, —
A ranar Asabar data gabata shafin sada zumunta na twitter ya rufe wasu asusun mutane biyu da aka same su da alaka wasu ‘yan leken asirin kasar Rasha, wanda kwamitin majalisar Amurka ke bincika.
A wani yukuri da gwamnatin Amurka ke yi don gano irin rawar da gwamnatin Rasha ta taka a lokacin zaben kasar Amurka a shekarar da ta gabata.
A ranar Juma’a da ta gabata kotun Amurka, ta kama wasu mutane 12 da laifin shiga yanar gizon jam’iyyar Democrat don daukar bayanai a shekarar 2016, wanda ake zargin kasar ta taimakama shugaba Donald Trump, darewa karagar mulki.
Shafin ya bayyana kulle asusun @DCLeaks da @Guccifer_2 dukkaninsu sun shiga cikin jerin sunayen da kwamitin majalisar Amurka take bincikar dangantar su da kasar Rasha.
Facebook Forum