Yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kai ziyarar aiki Kano, jiha mafi yawan jamaa a kasar.
A yayin ziyarar, shugaban ya aza harsashin aikin gina layin dogo na zamani daga Kano zuwa Kaduna wanda zai kasance ci gaba ne na wanda ya taso daga Abuja zuwa Kano.
Kazalika, shugaban ya bude hanyar gadar sama da gwamnati jihar Kano ta gina akan mahadar titinan Zoo Road da Zaria Road a cikin birnin Kano.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da kusoshin gwamnati da kuma ministan sufuri Rotimi Ameachi da sauran mukarraban gwamnatinn tarayya ne suka tarbi shugaban wanda ya sauka a Kano da karfe goma na safe agogon Najeriya.
Karin bayani akan: Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Shugaba Muhammadu Buhari, Kano, jihar Katsina, Nigeria, da Najeriya.
Bayan aza harsashin gina layin dogon, an tsara Shugaba Buhari ya kai ziyarar ban girma ga mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Yayin ziyarar, jami’an tsaro sun tare manyan titunan Kano, musamman wuraren da ayarin shugaban ya ratsa, al'amarin da ya zefa jama’a cikin mawuyacin hali wajen zirga-zirga saboda cunkoson ababen hawa.
Galibin jama’a dai a Kano ba su da masaniya dangane da ziyarar shugaban, la’akkari da cewa, hukumomi a Kano ba su kwarmata ziyarar ba.
Fadar shugaban kasar ta ce daga Kano, shugaban zai wuce jihar Katsina inda zai kaddamar da dam din Zobe da hanyar Dutsinma/Tsakiya mai tsawon kilomita 50.