Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mahara Sun Kashe Mutane 10 a Jihar Taraba


Wasu sojoji kenan ke kokarin tabbatar da tsaro a Nijeriya.
Wasu sojoji kenan ke kokarin tabbatar da tsaro a Nijeriya.

An kai hari kan wani bikin aure a Karamar Hukumar Gasol ta jihar Taraba, inda aka hallaka mutane 10.

Wasu mahara dauke da bindigogi da sauran makamai sun kai hari a garin Natirde da ke Karamar Hukumar Gasol ta jihar Taraba a cikin dare, inda su ka kashe mutane 10.

Wakilinmu a Shiyyar Adamawa Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito wani ganau na cewa a yayin wani bikin aure ne maharan su ka fantsamo da dare, su ka kashe na kashewa su ka raunata na raunatawa. Ya ce sun kai wadanda su ka sami raunuka wani asibiti a garin Mutum-Biyu.

Wakilin namu ya kuma ruwaito Kakakin ‘Yan sandan jihar ta Taraba ACP Joseph Kaji na cewa ‘yan sanda sun shiga sintiri tun daga garin Kasa, kuma duk wanda su ka kama shi da laifi zai dandana kudarsa.

Wani jigon dan siyasa mai tsokaci kan al’amura mai suna Usman Baborosombe ya danganta yawan tashe-tashen hankula da siyasa da kuma rashin adalci. Ya na mai kiran Kirista da Musulmi da su hada kai su sa cigaban yankinsu sama da komai.

Wasu Mahara Sun Kashe Mutane 10 a Jihar Taraba - 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG