Rahotannin bayan hare-haren da aka akai garuruwan Bauchi da Gombe a jihohin na Bauchi da Gombe na nuna cewa jimlar mutane 26 ne su ka hallaka sanadiyyar wasu fashe-fashe a wata kasuwar birnin Bauchi da kuma wata tashar mota a Gombe.
Wakilnmu a shiyyar Bauchi Abdulwahab Muhammad ya ruwaito kakakin ‘yan sandan Bauchi DSP Haruna Muhammad na cewa mutane 7 ne su ka mutu, 25 su ka sami raunuka. An sallami 6 daga cikinsu yayinda kuma har yanzu 19 na cigaba da yin jinya.
Shi kuma Kakakin ‘yan sandan jihar Gombe DSP Baja Attajiri y ace wadanda su ka mutu su 19 ne, banda wadanda su ka sami raunuka. Ya ce sun dau matakai kuma matakan na aiki. Sai dai ya yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro saboda a cewarsa batun tabbatar da tsaro ban a jami’an tsaro ba ne kawai na kowa da kowa ne.
Abdulwahab ya kuma ruwaito wani mai sharhi kan al’amuran tsaro mai suna Dr. Bawa Wase na cewa hanya mafi inganci ta tabbatar da tsaro ita ce a rinka binciken duk wani mai shiga muhimman wurare kamar su kasuwanni da makarantu da asibitoci da dai sauransu. Ya ce a binciki mutum ko an gan shi da kafa ko cikin mota kuma ko mi matsayinsa kuma komai mukaminsa. Ya ce ya kamata kuma binciken ya zama na dindindin ba kawai na ‘yan wasu sa’o’i ba.