Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashi a Tashar Dukku, Jihar Gombe


‘Yan kwana-kwana a wurin da bom ya fashe. (File Photo)
‘Yan kwana-kwana a wurin da bom ya fashe. (File Photo)

Karo na biyu ke nan ana tada Bom a tashar mota a jihar Gombe wanda ya janyo hasarar rayuka da raunata mutane da dama.

An sami labarin fashewar wani bom a tashar Dukku dake cikin garin Gombe a safiyar yau din nan, sai da ya zuwa lokacin da rahoton ya fito, ba a iya tantance adadin wadanda suka rasa rayukansu ko suka raunata ba.

Wani da abin ya faru a gaban idonsa, ya fadi cewa ba tare da bata lokaci ba jami’an tsaro suka isa wurin da ‘yan kwana-kwana, kuma yaga an dauki wasu da suka jikkata zuwa asibiti.

Wakilin muryar Amurka Abdulwahab Mohammed ya tuntubi sakataren hukumar bada agajin Red Cross a jihar Gombe Abubakar Yakubu, ya kuma tabbatar masa da cewa akwai wadanda suka mutu, wasu kuma sun raunata. Ya kuma ce sun taimaka wajen kai wasu asibiti.

Wannan shine karo na biyu da aka tada Bom a tashar mota a jihar Gombe.

Bom ya Tashi a Tashar Dukku, Jihar Gombe - 3'22"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG