Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kungiyoyin Najeriya Sun Tsayar Da Ranar 28 Ta Watan Mayu A Matsayin Ranar Yin Juyayin Yawan Kashe-kashe A Kasar


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kungiyoyin fafutika da na fararen hula daga sassa daban daban na Najeriya suka ware ranar 28 ta watan Mayu a matsayin ranar kalubalantar yawan kashe kashe da ake yi a kasar tare da yin juyayi

A karon farko, wasu ‘yan Najeriya sun kebe wata rana domin yin juyayi a daukacin kasar.

Masu fafutuka da kungiyoyin fararen hula daga sassan kasar, sun ware ranar 28 ga watan nan na Mayu domin su kalubalanci abin da suka kira “yawaitar samun tashe-tashen hankula a Najeriya.”

Gwamnatin Najeriya dai ba ta ware rana makamanciyar wannan ba, wacce za a yi juyayin wadanda suka mutu a rikice-rikicen kasar ba, wacce kungiyoyin na fararen hula suka jagoranta.

Amma a sassan kasar ta Najeriya, wacce ita ta fi yawan al’umma a daukacin nahiyar Afrika, jama’a sun taru a karon farko domin tunawa da wadanda suka mutu a tashe-tashen hankulan da ke faruwa.

Wani likitan a fanin kiwon Lafiya wanda ke fafutuka a Abuja, babban birnin kasar ta Najeriya, Felix Abrahams Obi, ya ce, Najeriya ta bi sahun sauran kasashen Duniya da ke bikin irin wannan rana ta tunawa da wadanda suka mutu.

Daya daga cikin jagororin wannan tafiya, wacce aka wa lakabi da “Enough is Enough” a turance, wato “abin ya isa haka,” ya ce, sama da mutane dubu uku aka kashe a wannan shekara.

Wannan sabuwar fafutuka na zuwa ne, yayin da yakin da gwamnatin Najeriyar ke yi da mayakan Boko Haram, ya shiga shekara ta goma.

Baya ga haka, akwai mummunan rikici tsakanin Fulani da makiyaya wanda rahotanni ke nuna cewa dumbin mutane kan mutuwa a kowane wata a sanadiyarsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG