A bara ne babban hafsan hafsoshin ruwan Najeriya Vice Admiral Ikwe Ibang, ya fadawa wani kwamitin majalisar wakilai cewa rundunar tana bukatar Dalar Amurka Bilyan daya da milyan dari uku domin ta sayi kayan aiki da zasu taimaka wajen kare kasar ta ruwa.
Yayinda take shirye-shiryen bukukuwan cika shekaru 62 da kafuwa rundunar sojojin ruwan Najeriya ta ce tana ci gaba da samun sabbin jiragen ruwan yaki tare da kara inganta wadanda take dasu yanzu.
Babban hafsan hafsoshin mayakan ruwan kasar Vice Admiral Ikwe Ibang shi ya ce kwana kwanan nan rundunar ta samu karin jiragen yaki daga kasar Faransa har guda shida. Za'a kaddamar dasu nan ba da jimawa ba. Ya zuwa yanzu cikin wannan shekarar rundunar ta samu jirage 373 ke nan wadanda suka taimaka wajen inganta tsaro a bakin ruwan Najeriya.
A cewar Vice Admiral Ibang rundunar na kara daukan matakai gaba biyu wajen cimma muradunta na samar da tsaro.
A cikin gida kuma rundunar tana anfani da injiniyoyinta wajen sabunta tsoffin jiragenta tare da kera wasu.
A cewar wani masanin tsaro Malam Kabiru Adamu, kara sabbin jiragen ruwan zai yi tasiri wajen samar da tsaro. Idan aka duba tsawon iyakar da Najeriya ke dashi ta ita ta ruwa, duk wani karin jiragen yaki ba zai yi yawa ba musamman idan aka yi la'akari da cewa can baya gwamnatoci da suka wuce sun yiwa rundunar rikon sakainar kashi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum