Gwamnatin Najeriya ta ce tana son tattaunawa da kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram, wadda aka dora wa alhakin kashe-kashe da dama a yankin arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwar gwamnati ta ce shugaba Goodluck Jonathan ya nada kwamiti mai wakilai 7 domin fara tattaunawa da kungiyar. Sanarwar ta ce shugaban ya nada wannan kwamiti a bayan da ya gana da shugabannin yankin da ake fama da wannan tashin hankali.
Har yanzu ba a ji martanin kungiyar game da wannan batun na tattaunawa ba.
Wannan shawara ta bude tattaunawa da kungiyar Boko Haram ta biyo bayan karuwar tashin hankalin da ya fi tsanani a Jihar Borno na arewa maso gabashin kasar, musamman Maiduguri babban birnin Jihar.
Kwanakin baya kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta ce an kashe mutane fiye da 140 a hare-haren bam na kungiyar Boko Haram a arewacin Najeriya kama daga watan janairun wannan shekara. Kungiyar ta Amnesty ta ce su ma ‘yan sanda sun kai hare-haren da suka yi sanadiyar mutuwar mutane a lokacin da suke mayarda martani ga kashe-kashen, ta kuma yi kira ga bangarorin biyu da su kawo karshen wannan tashin hankali.