Dattawan sun yi kiran ne domin tamkar kamar an samu gwamnatoci biyu ne a jihar yanzu. Kakakin taron dattawan dan kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP Isa Tafida Mafinda yace Danbaba ya fito daga kasarsu ne. Yace shi ne dan majalisar zartaswar jam'iyyar PDP da ta kafa gwamnati a Taraba. Mafindi yace "don Allah don Annabi a fuskanci gaskiya a rantsarda mataimakin gwamna wanda yake acting gwamna yanzu" Yace yau akwai wasu mutane dake kiran kansu sakatarorin gwamnati na bangaren Danbaba. Yace wannan bashi da kyau. Kamata ya yi a rantsar da mukaddashinsa. Idan Danbaba Suntai ya warke yana iya dawowa.
Dangane da ko addini da kabilanci sun shigo siyasar Taraba Mafinda yace a jiharsu babu wata kabila da ko Muslmai ne ko Kiristoci zalla. Ko a cikin Fulani akwai Kirista. Kan ko akwai gwamnati biyu yace su wadanna munafukan ke fadawa yan jarida cewa akwai gwamnati biyu amma su a Taraba ba haka lamarin yake ba.
Mukaddashin gwamnan Garba Umar yace gwamnati daya ce ita ce kuma ta Danbaba Suntai wadda shi yake gudanar da ita. Babu wata gwamnati kuma. Yace idan Allah Ya yarda ita ce zata cigaba har shekara maizuwa lokacin da zata zo karshe.