Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sojan Sudan Ta Kudu Ya Yi Wa Wata Mata Fyade


Wani ‘dan Sudan ta Kudu kuma limanin Angelican ya ce gwamnatin Sudan ta Kudu ba da gaske take ba wajen kama sojojin da suke wa mata da ‘yan mata fyade a kasar.

Limamin cocin wanda ya fito daga lardin cocin na Kudancin Sudan, Reverend Paul Yugusuk, ya ce ofishinsa ya bayar da rahotan wata mata mai ciki da wani sojan kasar mai ‘dauke da bindiga ya yi mata fyade a babbar hanyar Juba.

Yugusuk, ya fadawa shirin Muryar Amurka na turanci game da harkokin Sudan ta Kudu na South Sudan in Focus, cewa har yanzu jami’an soja basu kama sojan da ake zargi da aikata wannan ta’asa ba, wanda yanzu haka yake can watakila ma ya ci gaba da tsare mata da bindiga yana musu fyade.

A cewar limanin, sojojin da aka ajiye da mahadar Aju ne suka tsare matar da mijinta da karfin bindiga.

Cikin watan Fabarairun shekarar data gabata ne, shugaban kasa Salva Kiir ya baiwa ministan tsaro da babban hafsan sojojin kasar umarnin kashe sojojin da su kayi kisan kai ko fyade wa fararen hula a jihar Yei River.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG