Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Zimbabwe Ta Saki Ba Amurkiya Da Ta Tsare


 Martha O' Donovan
Martha O' Donovan

Wata Koti\u ta saki wata ba Amurkiya da ta zagi tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a wani shafin sada zumunci na intanet

A Zimbabwe, wata kotun kasar ta saki wata ba Amurkiya wadda ta tsare bisa zargin ta zagi tsohon shugaban kasar Robert Mugabe a shafin Twitter a bara.

Yau Alhamis ne kotun tayi watsi da karar, da ake zargin Martha O'Donovan, bayan da masu gabatar da kara suka gaza tsaida ranar da za'a fara sauraron karar.

A cikin watan Okotban bara ne aka kama O'Donovan, bayan da ta kira tsohon shugaban kasar dan sherkaru 93 da haifuwa a duniya "mai nuna son zuciya,kuma motsattse" a shafin Twitter. Da farko masu gabatar da kara sun yi mata cajin zagi da kuma raina shugaba Mugabe, kafin daga bisani suka kara da zargin yiwa Zimbabwe zagon kasa.

Makonni bayan da aka kama ta, sai shugaba Mugabe yayi murabus, bayan matsin lambar da sojoji suka yi na yin juyin mulki ba tare da an zubda jini ba, matakin da ya kawo karshen mulkin shekaru 37 daga hannun Mugabe.

Ita dai O'Donovan tana aiki ne tareda tashar Talabijin da ake kira Magamba TV, wacce ta kira kanta mai yada barkwanci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG