Nazari akan yaki da cututtukan shine makasudin taron kwamitin CCM dake da alhakin shawo kan cututtukan a Nijar. Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki a lamuran inganta rayuwar jama'a. Madam Sha'aibu Halimatu Sama'ila ita ce mataimakiyar shugaban kwamitin CCM, tace suna neman taimako akan yaki da tarin fuka da ciwon kanjamau ko sida da zazzabin cizon sauro.
Tace an umurci kowace kasa dake neman taimako ta yi babban muhawarar da za ta gayyato kungiyoyi da hukumomi dake fafutika da cututtukan a duniya suke kuma ba da taimako domin a ci gaba da yaki dasu. A wurin taron ne masu neman taimako za su fayyace irin taimakon da suke so da abun da za su yi da taimakon domin tabbatar da murkushe cututtukan nan uku..
Jin ta bakin kungiyoyi da jami'an hukumomi dake aiki a yankin karkara na da mahimmanci a tafiyar yaki da cututtukan saboda haka aka umurci jihohi su tattauna batutuwan. A cewar Madam Halimatu za'a fara taron a jihohin Diffa, Zinder da Maradi da Tillabery da Bosso. Dole ne a ji daga wadanda abubuwan suka shafa.
Bincike ya nuna cewa daga cikin mutane dubu dari mutum casa'in da uku ne ke fama da tarin fuka a Nijar yayinda aka gano kashi 60 cikinsu ne kawai ke zuwa asibiti neman magani, ke nan kashi arba'in din na ci gaba da baza kwayar cutar cikin jama'a.
Kawo yanzu kasar ta Nijar ta samu tallafin dalar Amurka miliyan dari biyu domin yaki da cututtukan.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum