Duk da cewar marasa lafiya a Afrika sun fi karacin shekaru, to amma kaso daya daga cikin dari sun rasa rayukansu ne bayan da aka yi musu aiki ko tiyata, in ka hadasu da rabin kaso daga cikin dari na mutuwa a fadin duniya sakamakon tiyata.
Wani marubuci Bruce Biccard na Jami'ar Cape Town yace "Wannan abun damuwa ne kwarai idan kaga yadda ake mutuwa sosai, in kuma ka duba yadda marasa lafiyar ke da karfi, kuma aikin da ake yi musu ba wani gagarumi bane".
Rashin ma'aikata da kayan aiki a Nahiyar baki daya, yana daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hakan a cewar marubuta a binciken da aka wallafa a wani kundi mai suna The Lancet.
Kungiyar wacce ta dauki masu binciken Afrika fiye da guda 30, sun dauki bayanan ayyukan tiyata da aka yi a asibitoci 247 a kasashen Afrika da suka hada da guda 25 daga Algeria zuwa Madagascar.
Binciken ya gano cewar akwai tsananin rashin likitoci masu tiyata a Afrika, Likitoci mata da kuma masu bada alluran barci. Binciken da aka yi a baya ya gano cewa, mutuwar marasa lafiya tana raguwa a wajen da yake da kwararrun likitoci 20 zuwa 40 a kowane rukunin jama'a guda dubu dari.
Amman a nahiyar ta Afirka, wannan binciken ya nuna cewa kwararrun ba su kai mutum daya a cikin kowane rukunin mutane guda guda dubu dari. Masu binciken na ci gaba da binciken neman mafita kan yadda za ayi a rage mutuwar marasa lafiya bayan anyi musu tiyata.
Sannan za kuma su mayar da hankali wajen ganin ko daidaita amfani da kayan aiki kan kayaddadun marasa lafiya ko wadanda suka fi fuskantar barazana zai taimaka wajen shawo kan matsalar..
Facebook Forum