Jami’an leken asiri na Somaliya, sun ce wani babban jagoran ‘yan tsagera na kasar, wanda aka yi shekara da shekaru ana nemansa, ya mika kansa ga gwamnati.
A yau lahadi da asuba, Mukhtar Robow Ali, wanda aka fi sani da sunan Abu Mansour, ya gana da wakilan gwamnati a makwancinsa dake wani kauye mai suna Abal a kudu maso yammacin Somaliya, daga bisani kuma aka dauke shi zuwa babban garin dake wannan yanki, watau Huddur.
Shine Moallim Nurow, shine kwamandan zaratan sojojin gwamnati a yankin kudu maso yammacin Somaliya. Kuma shi ya jagoranci tawagar gwamnati da ta samu isa sansanin Robow a jiya asabar.
Ya fadawa sashen Somaliya na VOA cewa ya gana da kwamandan a bakin daga a Abal, inda mayakan kwamandan da ya canja shekar da na al-Shabab suka shafe kwanaki suna gwabzawa.
Yace a bayan da suka gana ne suka yarda cewa zasu koma da shi garin Huddur. Yace ina tabbatar muku a yanzu haka yana Huddur, kuma ga ni tare da shi.
Robow ya sha rike mukamai kamar na kakaki, da ministan tsaro da kuma mataimakin shugaba a kungiyar al-Shabab. Yana daya daga cikin shugabannin kungiyar kalilan da suka rage wadanda suka samu horaswa tun farko a kasar Afghanistan.
Wani babban jami’in leken asiri na Somaliya yace Robow ya fadawa jami’an gwamnati cewa ya sauya sheka ne daga al-Shabab kuma yana son yayi aiki tare da gwamnatin Somaliya.
A yanzu haka dai, Robow yana da mayaka kimanin 400 a sansaninsa dake Abal, kilomita 18 a kudu da Huddur. Wannan zai iya zama canja sheka mafi girma da muhimmanci idan har shi da mayakan nasa suka koma bangaren gwamnati.
Facebook Forum