Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Rwanda Na Kan Gaba Da Kuri'u a Zaben Kasar


Paul Kagame
Paul Kagame

Shugaba Paul Kagame shine kan gaba da kuri’u a zaben shugaban kasar da aka gudanar, a cewar Hukumar zaben kasar.

A wani shirin gidan talabijin da aka watsa a kasar, babban sakataren hukumar zaben Rwanda, ya ce sama da kaso 80 cikin 100 na masu rijistar kada zabe a kasar, sun jefa kuri’unsu a yau Juma’a.

Cikin watan Yuli, Kagame ya fada a wajen wani gangamin kamfen cewa zaben shugaban kasar zai zamanto cikin tsari. Wannan babban rinjaye da shugaban ke da shi a zaben karon farko na nuni da cewa zai sami damar ci gaba da shugabancin kasar a karo na uku.

A babbar hedikwatar jam’iyyar Kagame ta R-F-P, dubban shugabannin siyasa masu goyon bayan shugaban ke kallon sakamakon zaben dake shigowa daga sassa daban daban na kasar ta wani katon majigi.

Kagame dai ya share shekaru 17 a kan karagar mulki izuwa yanzu. Wani zaben raba gardama da aka gudanar a shekarar 2015, ya baiwa Kagame damar tsayawa takarar shugabancin kasar har sai shekarar 2034.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG