Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kenya Jama'a Sun Fara Komawa Kan Harkokin Yau Da Kullum Bayan Bayyana Sakamakon Zabe.


Magoya bayan Ra'ila Odinga suka hura wuta domin toshe hanya a wata unguwar talaka a Nairobi.
Magoya bayan Ra'ila Odinga suka hura wuta domin toshe hanya a wata unguwar talaka a Nairobi.

Akalla mutane 9 sun mutu sakamakon zanga zangar a yankunan da 'yan hamayya suke da rinjaye.

A Kenya, bayan kammala yakin neman zabe mai tsawon gaske, 'yan kasar sun fara komawa ga "tsarin rayuwar da suka saba da ita ta yau da kullum," bayan da hukumomin kasar suka ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru kenyatta a zaman wand a ya lashe zaben kasar, domin fara mulki wa'adi na biyu bayan da ya doke dadadden abokin karawarsa a bnagaren 'yan hamayya Ra'ila Odinga.

Masu murna da 'yan zanga zanga kan sakamakon zabe suka fara daukar matakai har zuwa jiya Asabar.

Amma ba duka aka wanye lafiya ba. Rahotanni suka ce an harb aka kashe matasa tara a unguwar marasa gailhu da ake kira Mathare dake birnin Nairobi cikin dare.

Wani magidanci ya gayawa kamfanin dilancin labarai na Associated Press cewa, wani albarushi da ya baude ya kashe diyarsa yayinda take wasa da kawayenta a unguwar Matharen. 'Haka nan 'Yansanda sun harbe suka kashe mutane biyu a Kisimu tungar 'yan hamayya dake yammacin kasar a lokacin wata zanga zanga.

Amma Ministan cikin gida na kenya yace 'Yansand a suna mutunta doka da oda, domin ba laifi bane a gudanar da zanga zanga ta lumana.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG