Hukumomi sun fitar da wata sanarwa akan yadda wani mutum mai kokarin shirin yin sata ya ya kira su a waya, ya bar wayar a kunne har sai da ya gama bayyana yadda ya ke shirin dabarun yin fashi.
Jami'an 'yan sanda da ke unguwar Branchburg sun sami kira a tarho ranar ashirin da bakwai ga watan yulin wanna shekarar amma suka ce basu da tabbacin wurin da mai kiran yake amma da suka bincika, sun gano cewar lambar wayar ta wani matum mai suna Scott Esser, mai shekaru 42.
An kama mutumin a ranar larabar da ta gabata bayan zargin sa da ake yi da balle wani gida, da sauran fashin da aka yi a wasu wurare kusa da inda yake kuma duk a rana guda.
Hukumomi sun bayyana cewa dukkan fashin da aka yi, an yi su ne a ranar da Esser ya kira 'yan sandan domin bayyana masu irin shirin da ya ke yi na fashin. kuma an sa kudin belin sa akan kudi dalar Amurka dubu goma, kuma har yanzu ba'a sani ba ko yana da niyyar daukan lauyan da zai kare shi.