Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutum 17 A Mogadishu


Wani harin da ake zargin dan kunar bakin ya kai a kofar shiga wani Otel da ke kusa da wata mahada da ake kira K-4 da ake yawan hadahada a Mogadishu ya hallaka mutum 17 tare da jikkata wasu da dama.

Akalla mutum goma 17 suka mutu a tashin wani bam da aka dasa a cikin mota a Mogadishu a yau Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi na asibiti suka tabbatarwa da Sashen Somali na Muryar Amurka.

Daraktan babban asibiti na Mogadishu, Dr. Mohamed Yusuf, ya ce an kai karin wasu mutane 28 da suka ji raunuka asibiti.

Fashewar ta auku ne a lokacin da dan kunar bakin waken da ake zargi ya ta da bom din a kofar shiga wani Otel da ke kusa da wata mahada da ake kira K-4 da ake yawan hadahada a Mogadishu.

Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun fadawa sashen Muryar Amurka na Somali cewa motar an juya bayan ta ta kalli shingen duba ababen hawa na jami’an tsaro akan hanyar da za ta kai ga filin jirgin saman kasa da kasa na Aden Abdulle da ke babban Birnin kasar.

Sai dai kungiyar Al-shabab ta daukin alhakin kai wannan harin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG