Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Somaliya Ta Gudanar Da Zaben Da Ya Kamata A Gudanar Da Dadewa


White House building
White House building

Jinkiri a aiwatar da tsarin zaben Somaliya ya haifar da rikicin siyasa kasar. "Amurka ta damu matuka da matsalar zabe a Somaliya, wanda ke haifar da rashin tabbas na siyasa da ke barazana ga tsaro, kwanciyar hankali, da ci gaba a kasar," in ji Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken a cikin wata rubutacciyar sanarwa.

Bisa ga kundin tsarin mulkin Somaliya na wucin gadi, dole ne a gudanar da zaben ‘yan majalisu da na shugaban kasa a cikin wa’adin mulkin gwamnati na shekaru hudu.

A watan Satumbar 2020, Shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmaajo, da jami’an gwamnatin Tarayya kasar Somaliya biyar, sun amince da tsarin gudanar da zabe, amma aiwatarwa ya wargaje yayin da bangarorin ke zargin juna da neman yin amfani da tsarin wajen amfanin kansu. Yunkurin tattaunawa da aka yi ta yi da dama don warware matsalar zaben ya ci tura, wanda hakan ya haifar da rashin jituwar siyasa tsakaninsu ya tsaya cik.

Wa'adin Shugaba Farmaajo ya kare a ranar 8 ga Fabrairu, amma ya ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa, yayinda ya fake da shawarar majalisarta yanke na amincewa da yarjejeniyar tsarin zaben watan Satumba na 2020 na karawa’adin majalisar da kuma na shugaban kasarhar sai an kammala zabe.

Kawo yanzu Shugaba Farmaajo ya ki amincewa da bukatar bangaren ‘yan adawa da ya janye ikon gudanar da harkokin zabe da cibiyoyin tsaro, kamar yadda aka saba yi a duk lokacin da aka jinkirta sauya siyasa kamar na shekarar 2012 da 2016. Wannan ya kara tayar da hankali da yiwuwar rikice-rikice, yayin daa rangama tsakanin jami'an tsaron tarayya da kuma dakaru masu alaka da 'yan adawa, ta barke a Mogadishu a ranar 19 ga Fabrairu kafin da kuma lokacin zanga-zangar adawa da gwamnati.

Wannan lamari ne mai hatsari kuma dole ne a warware shi ba tare da bata lokaci ba.

Sakataren harkokin wajen Blinken ya ce "Muna kira ga shugabannin Tarayyar da na mambobin Somaliya da su ajiye manufofin siyasa, su sauke nauyin da ke wuyansu ga al'ummar Somaliya, kuma su amince da hanzarta gudanar da zabe na gaskiya da na kowa da kowa."

“Abin da ke faruwa a yanzu yana lalata ci gaban da aka samu ya zuwa yanzu, jinkiri ga sauye-sauyen da ake bukata cikin gaggawa don Somaliya ta ci gaba a kan hanyar ta na samun cikakken yafe bashin, kuma yana hana yaki da ta’addanci. Kasar Amurka na goyon bayan ‘yancin‘ yan kasar Somaliya na yin zanga-zangar lumana da nuna adawa kuma ta yi tir da amfani da tashe-tashen hankali daga kowane bangare. Muna rokon shugabannin Somaliya da su kiyaye makomar kasar tare da samun yarjejeniya don hanzarta gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki da na shugaban kasa.”

XS
SM
MD
LG