Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Fashe a Damaturu Ya Hallaka Mutane


Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Yobe
Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Yobe

Jiya da yamma wani bam ya fashe a Damaturu wurin da mutane suke kallon kwallon kafa ya kuma rutsa da mutane da dama

Bam da ya tarwatse a wurin da mutane ke kallon kwallon kafa na gasar cin kofin duniya ya rutsa da mutane da dama.

Wani mazaunin garin Damaturu fadar gwamnatin jihar Yobe da ya zanta da Muryar Amurka ya tabbatar da fashewar bam din a gidan kallo. Yace bayan sallar magariba da ya dawo gida sai aka kirashi aka fada masa cewa wani bam ya fashe a can bakin kasuwa.

Sabili da gidan wansa yana gaf da ginin gidan kallon sai ya kirashi ta waya. Shi wan nasa ya shaida masa lallai bam ya fashe yayin da shi da dansa suke zaune a kofar gidansa. Bayan fashewar sai yaji kamar ruwa na zubowa daga kansa. Da ya taba sai ya ga jini. Dansa kuma dake zaune shi ma kafarsa ta karye.

Yayin da ya duba gefensa sai ya ga gawarwaki da hannuwa da wasu sassan jikin mutane. Sabili da halin da shi kansa yake ciki bai iya sanin adadin wadanda suka rasa rayukansu ba ko kuma yadda ginin gidan kallon yake. Sai yau za'a san adadin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikata.

Da zara an samu cikakken bayani zaku ji ku kuma karanta daga Muryar Amurka.

Ga zantawar da aka yi da Alhaji Isyaku Damaturu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG