Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama ‘Yan Arewacin Najeriya Fiye da Mutane Dari Hudu


'Yan Arewa
'Yan Arewa

Mutane da aka kama a cikinsu akwai mata takwas.

An kama ‘yan arewacin Najeriya fiye da mutane dari hudu a cikin motar safa-safa wadanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne, a jihar Abia kudu maso gabashin Najeriya.

Mutane da aka kama a cikinsu akwai mata takwas,a kuma kama sune a hanyar Enugu zuwa Port Harcourt a cikin motoci talatin da uku.

Comrade, Ahmed Muhammad Bunza, shugaban cibiyar habaka demokradiya a Najeriya, yace ‘yan arewa na wahala masamman a kudancin Najeriya.

Inda ya bada misali da cewa an kama ‘yan arewa a jihohin Legas, Benue da Abia a watanin da suka wuce kuma aka maida su arewacin Najeriya, Yace wannan na nuni da cewa ‘yan arewa kawai ake wa wannan.

Muhammadu Bunza, yace bisa ga alkalluman gwamnatin taraiya mutane dubu goma sha biyu ne suka mutu dangane da mummunar aika-aikan ‘yan Boko Haram.

Yana mai cewa kimanin mutane dubu tara da dari bakwai a ciki duk kansu ‘yan arewa ne kuma masu bin addinin Islama.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG