Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Yola


'Yan gudun hijira a Yola jihar Adamawa
'Yan gudun hijira a Yola jihar Adamawa

Yayin da yake jawabi wakilin yace ya lura cewa yara da dama suna fama da rashin abinci mai gina jiki da rashin koshin lafiya da ciwon ido.

Wakilin majalisar yayi alkawarin yin kokarin dakile yaduwar ciwon ido cikin mutanen dake sansanin na 'yan gudun hijira. Yayi jawabinsa ne ga mutane 275 wadanda sojojin Najeriya suka ceto daga dajin Sambisa inda 'yan Boko Haram da suka sacesu suke tsare dasu.

A tawagar wakilin majalisar dinkin duniya akwai hukumar kai dokin gaggawa da aka sani da suna NEMA da kuma likitoci kwararru a fannoni daban daban wadanda suke aiki kafada da kafada wajen kulawa da lafiyar 'yan gudun hijiran..

To saidai ziyarar hukumar NEMA zuwa sansanin na Malkohi a karkashin darakta dinta na kasa Alhaji Sani Sidi ya gamu da fushin 'yan gudun hijiran wadanda suka dade a sansanin. Su dai wadan nan suna neman a mayar dasu garuruwansu tunda sojoji sun kwatosu sun kuma kakkabe duk 'yan ta'adan dake yi masu barazana. Su dai 'yan gudun hijiran basu da sukunin komawa garuruwansu sai dai an taimaka masu.

Suna son su koma garuruwansu domin su je su shiryawa daminar bana. Mutanen sun yi korafin cewa an yi watsi dasu. Basu da sabulun wanka ko wanki sai dai sun fita bara. Manyan 'ya'yansu an kaisu makarantu an barsu suna fama da kananan yara.

Da yake mayarda martani daraktan NEMA ya nemi su hada kai dasu. Yace zasu yi masu sutura kuma likitoci zasu dinga kula dasu.

To saidai 'yan gudun hijiran suna kokawa da karancin abinci. Wasu a dakuna kimanin arba'in sai da suka kwana ba abinci jajiberen wannan ziyarar.

Ga rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG