Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BOKO HARAM: Menene Matsayin Matan Da Aka Ceta Da Ciki


Wani Sojan Najeriya Yana Magana Da Wasu Da Aka Ceto
Wani Sojan Najeriya Yana Magana Da Wasu Da Aka Ceto

Sojojin Najeriya suna ta sake kwato wasu mutanen da wasu 'yan boko haram ne suka yi garkuwa da su. To sai dai matsalar da ta biyo baya ita ce, wasu matan da aka ceto an same su dauke da juna biyu.

Game da matan da sojojin Najeriya suke ta kwatowa daga dajin Sambisa da makamantan wuraren da ‘yan Boko Haram suka mamaye a da, wadansu daga matan an same su da ciki da suka samu sakamakon fyade ko makamancin haka.

Mutane da yawa na ta tababar ko za’a iya barin cikin da suka dauka ko a’a? Wannan ce tasa Jummai Ali ta Muryar Amurka ta tuntubi wasu Limaman Musulmi da Kirista don jin yadda abin yake a addinan ce kasancewa addinan biyu ne yawanci mutanen Najeriya ke bi.

Dukkanin Malaman addinan guda biyu ba wanda ya bada goyon bayan zubar da cikunnan don kuwa a addinance hukuncin kisan kai ne. Duk da yake dai sun nuna cewa za’a iya zama da manyan limamai a sami wata fatawa da zata zamo mafita ga lamari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:01 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG