Dr Khalid Abubakar Aliyu sakataren Jama'atul Nasril Islam ya ce bayan mika wuya ga Ubangiji da yadda da abubuwan da Ya kaddara sun shiga cikin wani halin firgici da matukar tashin hankali. Cikinsu ya kadu kwarai domin irin wannan abun ya faru da can sai kuma gashi ya sake faruwa. Ya ce sai abun yana son ya fassara masu cewa kamar wani abu ne shiryayye. An kashe Malam Mai Shiyya na Sokoto wanda har yanzu suna jinshi a zuciyarsu sai kuma gashi wannan ya sake faruwa ga Sheikh Albani duk malaman addinin Musulunci kadai. Kila wannan barazana ce domin malamai su daina karatu su kuma daina fadin gaskiya. Na biyu ko kuma ana tauna tsakuwa ne domin aya ta ji tsoro. Watakila wani bangare ne na siyasa ko kuma wani abu mai tada hankali. Ya ce suna cikin tashin hankali kuma suna kira ga gwamnatin kasar wadda Allah ya dorawa kare lafiyar 'yan kasar da kare dukiyarsu da kare mutuncinsu na yin kowane addini ba tare da tsangwama ba. Daga karshe ya ce suna nazarin yadda zasu tunkari lamarin.
Matakin farko shi ne dole gwamnati ta tashi ta tsaya akan jiga-jiganta ta tabbatar da tsaro da kariya ga duk 'yan Najeriya. Yanzu malamai na anfani da abun da suke dashi ne domin yin wa'azi da wasu harkoki. Ba wani kudi ake basu ba sai dai wadanda suke da hali su taimaka masu.