Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa, sabon tsarin da babban bankin kasar ya fitar na kayyadade adadin kudin da za a cire a banki ya fara aiki.
A bara, babban bankin na CBN ya sanar da cewa naira dubu 500 mutum guda zai iya cirewa a mako sannan kamfanoni kuma miliyan biyar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa, yayin da wasu masu cire kudin sun ankara da fara aiwatar da tsarin wasu kuwa sai da ma'aikatan bankuna suka yi musu tuni.
Dokar ta fara aiki ne a ranar Litinin 9 ga watan Janairu, kuma rahotanni sun yi nuni da cewa bankuna sun fara bin umarnin.
Da farko babban bankin na CBN ya kayyade kudaden da mutum zai iya cirewa a mako akan naira dubu 100, sannan kamfanoni kuma za su cire naira dubu 500.
Sai dai bayan korafe-korafe da mutane suka yi da kuma shiga tsakanin da majalisar dokokin Najeriya ta yi, CBN ya kara adadin.
Bankin na CBN ya ce ya dauki matakin ne domin a dora Najeriya bisa turbar yin hada-hadar kudaden ta yanar gizo.