Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harris Da Trump Sun Yi Ta Caccakar Juna A Wata Muhawara Me Cike Da Tarihi


Miliyoyin Amurkawa ne suka kali wannan muhawara da watakila za ta kasance daya tilo a wannan lokacin yakin neman zabe.

Zaton da ake yiwa mahawarar tsakanin 'yan takarar shugabanci Amurka; tsohon shugaban kasa Donald Trump da Mataimakiyar Shugaban Kasa Kamala Harris ta tabbata, kasancewar dukkaninsu sun yi ta bankado abubuwan da suke zargin gazawar juna ne tare da burukan da suke nufin cimma idan aka zabe su.

A jawabinta na bude mahawarar, mataimakiyar shugaban kasa kamala harris tace, "ina da kyakkyawan yakinin cewa amurkawa na bukatar shugaban daya fahimci mahimmancin hada kawunansu, na san cewar abubawan da muka yi tarayya akai sun rinjayi wadanda suka rabamu. Kuma nayi muku alkawarin zama shugaba ga ilahirin Amurkawa."

Da yake magana akan hauhawar farashin kayan masarufi, Trump yace "a zamanina ba'a samu hauhawar farashi ba, babu ko kadan. Su keda matsalar mafi girman hauhawar farashi, ina zaton wanda ba'a taba gani ba a tarihin kasarmu. Ban taba ganin zamanin daya fi wannan muni ba. jama'a basa iya fita su sayi hatsi ko nama ko kwai da sauran kayan masarufi."

Dukkanin 'yan takarar 2 sun bayyana ra'ayoyinsu game da kudirin dokar zubda ciki da aka jima ana takaddama akansa, inda Trump yace "tsawon shekaru 52 suka shafe suna kokarin kakaba kudirin nan mai lakabin"roe v. wade" akan jihohin kasar nan amma sakamakon kaifin basira da jajircewar alkalan kotun kolinmu guda 6 mun iya dakile hakan. Yanzu, na amince da sharudan fyade da samun ciki sakamakon zina tsakanin 'yan uwa da kokarin ceto rayuwar uwa da aka kebe na dokar. Ina matukar goyon bayan abinda Ronald Reagan yayi da kuma wanda kaso 85 cikin 100 na 'yan jam'iyyar Republican suka yi na amincewa da kebe wani sashe na dokar, hakan nada mahimmanci, mun yi nasarar tabbatar da hakan kuma yanzu jihohi na kada kuri'a akansa a karon farko. Zaku gani, wannan batu ne daya jima yana raba kan al'ummar kasarmu tsawon shekaru 52."

A yayin da kamala harris tayi amannar cewa "ba sai mutum yayi watsi da imaninsa ko abinda ya yarda dashi ba kafin ya amince. Bai kamata gwamnati ko Donald Trump su gayawa mace abinda zata yi da jikinta ba" sannan tayi zargin cewar babu wani shirin da Trump din keda shi akanku. idan kuka yi nazarin tsarinsa na tattalin arziki, babu komai in banda yin rangwamen haraji ga attajirai."

Sai dai tsohon shugaban kasar yayi martani da cewar "babu wanda bai san cewar ke (kamala harris) 'yar gurguzu ce mai ra'ayin makisanci."

Miliyoyin Amurkawa ne suka kali wannan muhawara da watakila za ta kasance daya tilo a wannan lokacin yakin neman zabe.

Wannan fafatawar ta kasance makonni takwas kafin ranar 5 ga watan Nuwamba da za a yi zabe amma saura ‘yan kwanaki kadan kuma kafin fara zaben a wasu jihohi 50 na kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG