Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Usain Bolt Ya Nuna Goyon Baya Ga ‘Yan wasan Ingila Da Suka Barar Da Fenariti


Usain Bolt
Usain Bolt

“Sun sha matukar wahala. Bai dace yadda aka rika zaginsu a shafukan intanet ba. Na san akwai zafi ka ga tawagarku ta sha kaye, amma bai dace a ce ana zaginsu ba."

Fitaccen dan wasan tseren kafa na kasar Jamaica Usain Bolt ya nuna goyon bayansa ga ‘yan wasan da suke bore a gasar wasanni ta Olympics da ake yi a Tokyo kan matsalar wariyar launin fata da ake nunawa a fagen wasanni.

Bolt wanda har ila yau yeke buga kwallon kafa, ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ‘yan wasan Ingila suka fuskanci wannan matsala ta wariyar launin fata bayan wasan karshe da aka fitar da Ingila a gasar Euro 2020.

“Sun sha matukar wahala. Bai dace yadda aka rika zaginsu a shafukan intanet ba. Na san akwai zafi ka ga tawagarku ta sha kaye, amma bai dace a ce ana zaginsu ba, hakan ba daidai ba ne. Na yi farin ciki da na ga wasu mutane sun fito suna Allah wadai da lamarin, ana kuma shirin ladabtar da wadannan mutanen.” Bolt ya ce kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Ya kara da cewa, “kamata ya yi a ce ‘yan wasa suna da karfin da za su bayyana abin da suke so, ko abin da suke so su ga an samar da sauyi akai

“A matsayinmu na ‘yan wasa, mun san abin da muke so da zai kara mana kaimi da jin dadin abin da muke yi.”

A wasan karshe na gasar cin kofin Euro 2020 da aka yi a ranar 11 ga watan Yuli, ‘yan wasan Ingila Marcus Rashford, Jadon Sancho da Bukayo Saka, sun bararwa da Ingila fenariti lamarin da ya ba Italiya damar lashe kofin gasar. Dukkan ‘yan wasan bakaken fata ne.

Hakan ya sa wasu suka shiga shafukan sada zumunta suka yi ta cin zarafinsu, musamman Saka wanda ya barar da fenaritin karshe da ta ba Italiya damar lashe kofin.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG