Najeriya ta buga wasan ne da ‘yan wasa shida da ke karawa a gasar kwallon kwandon Amurka ta NBA – mafi aksarinsu ba sanannu ba ne.
Amma tawagar Amurka ta kara da Najeriyar dauke ‘yan wasa da dukkansu suna karawa a gasar NBA wadanda duk kusan fitattu ne.
Masu sharhi na cewa ba da haka Amurka ta so ta fara a gasar ta Olympics ba, bayan da Najeriyar ta shammace ta.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito, ita kanta Najeriyar ta kare wasan cikin mamaki ganin nasarar da ta samu akan zakarun duniya na wasan kwallon kwando
“Mun buga wasan ne kawai don mu yi gogayya da su,” in ji dan wasan Najeriya, Gabe Nnamdi, wanda ke amsa sunan Gabe Vincent a gasar NBA tare da kungiyar Miami Heat kamar yadda AP ya ruwaito.
Ya kara da cewa, “mun san abin da wasan kwallon Amurka na NBA ke nufi a duk fadin duniya, da kuma irin kimar da suke da shi na tsawon lokaci.”
Ana sa bangaren, mai horar da ‘yan wasan Amurka, ya jinjinawa tawagar ta Najeriya game da irin wasan da ta buga.
“Ina ga tawagar ‘yan wasan Najeriyar ta buga wasa da karfin gaske, ta yi abin a zo-a-gani, sannan zun zura kwallaye masu maki uku da dama. Ya kamata a jinjina masu” In ji Gregg Popovich.
Ita dai Najeriya ta taba shan kaye a hannun ‘yan wasan Amurka a wasannin Olympics na 2012, sannan sun kuma shan wani kayen a hannunsu shekara hudu bayan haka.