Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fuskantar Matsalar Kwashe Marasa Lafiya Daga Gaza Domin Yi Musu Jinya


Wani asibiti a Gaza
Wani asibiti a Gaza

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sunyi gargadin cewa, aikin kwashe marasa lafiya daga yankin da yaki ya daidaita a Gaza na neman dishewa, lamarin dake jefa rayuwar dubban mutane da ya hada da yara kanana cikin hadari, da cututtuka, da jikkata, da basa iya samun kulawar da suke bukata.

Mai Magana da yawun asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya James Elder, ya shaidawa maneme labarai a ranar Juma’a a Geneva cewa, yaro daya kacal ake iya fita da shi daga Gaza a duk rana zuwa asibiti, lamarin da idan yaci gaba a irin wannan tafiyar hawainiyar, Kenan za’a shafe shekaru sama da 7 kafin a kwashe yara 2500 dake bukatar kulawar gaggawa.

Yace, sakamakon hakan yara na mutuwa a Gaza, ta yadda ikon Allah kadai ke kare rayuwar yaran da suka rika tsallake rijiya da baya a irin luguden bama bamai da alburusan da ake yi, ya rika kange su daga samun ficewa daga Gaza, domin samun kulawar da suke bukata cikin hanzari domin ceto rayuwar su.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ruwaito cewa marasa lafiya su 15, 600 ke bukatar a fita dasu domin yi musu jinya, inda mutane 5,138 kacal aka iya fitarwa ya zuwa yanzu. Kusan rabi daga cikin su na fama ne da cutar kansa, kashi 40% na fama da raunuka da suka samu sakamakon yakin, da wasu 200 dake fama da cutar koda. Hukumar lafiyar ta duniya tace, marasa lafiya 231 aka samu fita dasu tun ranar 7 ga watan Mayu.

Mai magana da yawun asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Elder, ya lura da cewa, kimanin yara 296 dake bukatar ayiwa jinya ne aka rika fitarwa a duk wata tun daga watan Janairu zuwa 7 ga watan Mayu, sakamakon barin wuta ta kasa da aka rikayi ta kasa, inda tun daga nan adadin yaran da aka rika fita dasu jinya ya rika yin kasa zuwa yara 22 kacal a duk wata.

Ya kara da cewa, yara 127, dake fama da razana a kan su, ko yankewar wani sassa na jikin su, da cutar sankara wato kansa, da matsanancin karancin rashin abinci mai gina jiki ne aka bari su fita tun bayan da aka Rufe birnin Rafah.

Wakilin hukumar lafiyar ta majalisar dinkin duniya a yankin da aka mamaye na palasdinawa, Dr Rik Peeperkorn, yace tabbas halin da ake ciki a yankin na Gaza na bukatar kyakkyawa kuma ingantaccen tsari.

A wata ganawa da aka yi da shi ta video daga Gaza, yayi waiwaye cewa, kafin barkewar rikicin a shekara gudan da ta gabata, tsakanin marasa lafiya 50 da 100 ne ake turawa jinya daga Gaza zuwa gabashin birnin kudus da yankin gabar kogin Jordan, daga ciki kashi 40% na marasa lafiyar yara ne, da mata da ma maza dake fama da cutar kansa, da sauran cututtuka dabam dabam.

Peeperkorn yace, dole ne a dauki marasa lafiya dake cikin yanayi mai tsanani da yawan su ya kai tsakanin 12,000 da 14,000 a jirgin saman daukar marasa lafiya zuwa wajen Gaza, kuma ananan ana ta bada himma domin samun yuwuwar hakan.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Tsofaffi Ke Fama Da Lalular Yanar Ido A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG