Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasanta da za su fafata da abokanan hamayyarasu na Liverpool a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.
A ranar Talata Madrid za ta gwada kaiminta da Liverpool a wasan farko na zagayen quarterfinals a filin wasa na Estadio Alfredo Di Stefano da ke birnin Madrid a kasar Spain.
Karin bayani akan: Real Madrid, Liverpool, Sergio Ramos, da Benzema.
Za ta je wasan ne da zaratan ‘yan wasa 21, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Litinin.
Ga jerin ‘yan wasan:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Altube
Masu tsaron baya: E. Militao, R. Varane, Nacho, Marcelo, Odriozola da F. Mendy
‘Yan wasan tsakiya: Kroos, Modric, Casemiro, Valverde, Isco da Arribas
Masu kai hari: Benzema, Asencio, Lucas V., Vini Jr., Mariano da Rodrygo.
Yanzu haka, dan wasan tsakiya Fede Valverde ya dawo daga jinya, amma Eden Hazard, Sergio Ramos da Dani Carvajal ba za su samu damar buga wasan ba.
Masu fashin baki sun ce babban kalubalen da ke gaban Madrid shi ne, yadda za su kare bayansu lura da cewa ‘yan wasan Liverpool sun kware wajen kai hari.
UEFA Da FIFA Ba Sa Kyautawa ‘Yan Wasa - Pep Guadiola