Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos, ba zai samu damar buga wasan quarter-final na cin kofin gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA ba, wanda za a fara a mako mai zuwa.
Cikin tausasan kalamai dan wasan ya shiga shafinsa na Instagram a ranar Alhamis ya ce, ya samu rauni a agararsa.
“Babu abin da ya fi kona min zuciya, kamar a ce ba zan iya taimakon kungiyata ba, a lokacin da aka fi bukata ta, a wadannan wasannin masu zafi” Ramos ya rubuta da harshen spaniya a shafinsa na Instagram.
Hukumar UEFA ma ta wallafa labarin a shafinta na Twitter inda ta ce dan wasan ya samu rauni a da ya shafi jijiyar kafarsa.
A ranar 6 ga watan Afrilu, Real Madrid za ta gwada kaiminta da Liverpool a zagayen farko na wasannin kusa da na karshe a gasar ta UEFA.
Dan shekara 35, Ramos ya samu raunin ne a wasan da ya bugawa kasarsa da Kosovo a ranar Laraba.
Rahotanni daga kasar Andalus sun ce, Ramos zai kwashe wata daya yana jinya, abin da ke nufin ba zai samu damar buga wasansu da Liverpool ba a zagayen ‘yan-takwas da za a fara a mako mai zuwa a gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA.