ABUJA, NIGERIA - Sai dai wakiliyar Muryar Amurka a Abuja Medina Dauda ta ziyarci gidan kaninsa, wanda suke uwa daya, uba daya mai suna Dr. Dauda Tsalhatu Gowon domin fayyace lamarin.
Dr. Dauda Tsalhatu Gowon ya bayyana wa Muryar Amurka cewa tun da sanyin safiyar ranar Litinin ne ya fara samun kira ta waya, ana ta yi masa ta'aziya wai kan rasuwan yayansa Janar Yakubu Gowon.
Dauda ya ce abin ya ba shi mamaki, domin idan an samu irin wannan mummunan labari, ai daga wurinsa ne ya kamata labari ya fito cewa 'yayan nasa ya rasu, amma wannan sai ya zama daga waje ake kiransa ana masa gaisuwa.
Ko da yake, Dauda ya ce sai da suka yi magana ta waya da yayan nasa, Janar Yakubu Gowon ne hankalinsa ya kwanta domin Janar Yakubu Gowon suna hutu da iyalinsa a Ingila a yanzu haka.
Dauda ya ce su 11 aka haifa a gidansu, shi Dauda shi ne na goma a ayarin 'ya'ya a gidansu na Wusasa Zaria, inda iyayensu, suka yi rayuwarsu kafin su bar duniya.
Dauda ya ce a yanzu haka suna shirye-shiryen yi wa Janar Yakubu Gowon addu'o'i na murnar cika shekaru 89 a duniya, a ranan 19 ga wannan wata na Oktoba na shekaran nan da muke ciki.
An haifi Janar Yakubu Gowon a ranan 19 ga watan Oktoba na shekara 1934 ne.
Dauda ya ce wani ‘dan kudu maso kudu kuma tsohon Shugaban kungiyar malaman jami'o'i mai suna Gowon Edoumekumor shi ne wanda ya rasu a ranan 9 ga wannan wata na Oktoba, kuma ba ‘dan'uwansu ba ne.
A cewar Dauda, suna ne ya zo kusan daya, shi ya sa mutane suka rude daga jin sunan Gowon.
Dauda ya ce suna yi wa babban yayansu Janar Yakubu Jack Gowon addu'ar fatar alheri, tsawon kwana cikin koshin lafiya da walwala.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna