Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Saman Najeriya Amaechi Ya Rasu


Dakin ajiyan gawa
Dakin ajiyan gawa

Tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.

A cewar wata sanarwa daga dangin mai dauke da sa hannun Ezeana Tagbo Amaechi, tsohon ministar ya mutu ne da sanyin safiyar yau Talata, 1 ga Nuwamba, 2022.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Tare da cikakken ikon Allah, iyalan Ume Amaechi, Ezeana Ihinede da kuma ‘yan’uwan Umu Mmara na Amihe Ukpor da ke karamar hukumar Nnewi ta Kudu a Jihar Anambra, suna sanar da cewa, fitaccen dan mu, babanmu da kuma kakarmu ya rasu cikin kwanciyar hankali. Cif Mbazulike Amaechi (Dara Akunwafor), mai kishin kasa kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama na Tarayyar Najeriya, ya bar duniya da sanyin safiyar yau 1 ga Nuwamba, 2022."

“Muna godiya ga Allah bisa rayuwar da ya yi, da rayukan da ya taba da kuma hidimarsa ga Allah da kasa. Muna rokon ku da ku sanya mu cikin tunaninku da addu’o’inku a wannan lokaci.”

Har zuwa rasuwarsa, Cif Amaechi, wanda ya fito daga kauyen Amihe da ke Ukpor, a karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, ya kasance mai kishin kasa kuma kafin rasuwarsa, shi kadai ne ya rage dan kungiyar Zikist a raye.

XS
SM
MD
LG