Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJER: Shugaban Jam'iyar PNA Al'umma Sanoussi Jackou Ya Rasu


SANOUSSI JACKOU
SANOUSSI JACKOU

Allah ya yiwa shugaban jam'iyar PNA Al'umma Sanoussi Jackou cikawa a yammacin jiya litinin a asibitin kwararru na Birnin Yamai.

Marigayi ya rasu ya na da shekaru 82 a duniya ya yi gwagwarmaya tun a zamanin da yake dalibi, ya kuma kalubalanci gwamnatocin sojan da suka yi mulki a Jamhuriyar Nijer, lamarin da ya ba shi damar rike mukamin minista sau tari a gwamnatocin fararen hular kasar, sannan ya yi dan majalisar dokokin Kasa, da kuma mataimakin kakakin majalisa sannan dan gidan sarautar garin kornaka a jihar Maradi ne.

SANOUSSI JACKOU
SANOUSSI JACKOU

Har i zuwa jiya litinin Sanoussi Djackou na rike da mukamin mashawarci na musamman a fadar shugaba Mohamed Bazoum.

Nan gaba za a bada sanarwar lokacin da za a yi masa jana'iza.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG