A cikin sanarwar da ‘ya’yanta su ka fitar, sun bayyana mahaifiyarsu Ivana a matsayin tsayayyar mace mai kwazon gaske.
Shi ma tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya bayyana jimamin mutuwar matar sa ta farko a shafinsa na sada zumunta Truth Social inda ya bayyana cewa,
"Ina matukar bakin cikin sanar da duk wadanda suke kaunarta, wadanda suke da yawa, cewa Ivana Trump ta rasu a gidanta da ke birnin New York. Mace ce mai ban mamaki, kyakkyawa, kuma hazika, wacce ta yi rayuwa mai kyau da ban sha’awa. Abin alfaharinta da farin cikinta su ne 'ya'yanta uku, Donald Jr., Ivanka, da Eric. Ta yi alfahari da su. Duk muna alfahari da ita. Allah ya ji kan ki, Ivana!"
Rahotanni na nuni da cewa, an kira ‘yan sanda zuwa gidan Ivana da ke unguwar Manhatan a birnin New York, inda su ka tarar da ita a kasa kusa da matakalar hawan bene a mace. Sai dai I zuwa lokacin rubuta wannan rahoton ba a sanar da sanadin mutuwar ta ba.
An haifi Ivana Trump, née Zelnickova, a ranar 20 ga watan Fabrairu, 1949, a Czechoslovakia, Kafin auren tsoshon shugaban kasar Amurka Donald Trump, ta auri wani dan kasar Australiya mai suna Alfred Winklmayr, a shekara ta 1971, da ya bata damar zama ‘yar kasar Austriya ta fice daga kasar ta ta asali Czechoslovakia da ke karkashin mulkin kwaminisanci. Aurensu ya mutu a shekarar 1973.
Bayan rabuwa da Donald Trump, Ivana ta yi aure sau biyu sai dai duka biyu suka mutu cikin shekaru biyu. An yi bukin auren ta na uku da Riccardo Mazzucchelli wani dan fitaccen dan kasuwa dan asalin kasar Italiya a gidan shakatawa na kawa na tsohon shugaban kasar Trump at his Mar-a-Lago dake Florida da 'yarta Ivanka Trump ta yi mata babbar kawar amarya.
Ivana ta yi fice a fannin tallar kayan kawa. Ta gamu da Donald Trump a birnin New York a shekata ta 1976 lokacin da ta yi wani balaguron yin tallan kayan kawa. Sun yi aure shekara guda bayan saduwarsu. Suka kashe aure a shekara ta 1992 bayan sun haifi ‘ya’ya uku.
Ivana Trump ta yi fice wajen sayar da kayan kawa da tallata tufafin kawa da kayan kwalliya.
Ivana ta rasu ta bar mahaifiyarta, da ‘ya’ya uku da kuma jikoki 10.