An haife shi a Masar a shekara ta 1926, Qaradawi ya shafe tsawon rayuwarsa a kasar Qatar, inda ya zama daya daga cikin manyan malaman Musulmi mabiya Sunna da kuma fada a ji a kasashen Larabawa sakamakon bayyanarsa a kafar yada labarai ta Aljazeera ta kasar Qatar akai-akai.
"Mai girma Imam Youssef al-Qaradawi, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bayyana rukunan Musulunci da kuma kare al'ummarsa, ya koma ga Ubangiji" a cewar wata sanarwa da aka fitar a shafin Twitter inda aka bayyana rasuwarsa, cewar ya yi fama da rashin lafiya.
Wa'azin Qaradawi ya yi matukar tasiri kan akidu masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyin al-Qa'ida suke da shi, tare da tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda a wasu sassan yankin. Ya yi matukar suka ga shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da kuma mahukuntan Saudiyya, lamarin da ya kara rura wuta tsakanin kasashen da Qatar.
Wata kotu a Masar ta yanke masa hukuncin kisa duk da rashin bayyanar sa a shekarar 2015 tare da wasu shugabannin kungiyar Ikhwan. Hukumomin Masar sun tsare ‘yarsa bisa zargin ta’addanci a shekarar 2017 har zuwa shekarar 2021, yayin da ake ci gaba da tsare surukinsa, in ji lauyansu. Sun musanta zargin.
A wani taron karramawa, shugaban masu kishin Islama na Tunusiya Rached Ghannouchi ya bayyana Qaradawi a matsayin "mai biyayya ga ka'idar daidaitawa a cikin wannan addini mai girma."
Sai dai kuma wasu masu amfani da shafukan sada zumunta da suka fito daga Masar da Saudiyya da sauran kasashe sun yi murnar rasuwarsa tare da zarginsa da haddasa fitina tsakanin kasashen Larabawa.