Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Mijin Diezani Allison- Madueke Ya Nemi Kotu Ta Hana Ta Amfani Da Sunanshi


Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani
Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani

Tsohon hafsan mayakan ruwa, Admiral Allison Madueke mai ritaya wanda kuma ya yi gwamna a jihohin Anambra da Imo ya bukaci kotu ta umarci tsohuwar Minister Diezani Allison- Madueke ta daina amfani da sunan shi, ta koma amfani da sunan mahaifinta Agama domin daina bata mashi suna.

Tsohon mayakin ruwan mai tiraya ya shigar da kara yana neman tsohuwar Ministar ta daina amfani da sunanshi ne sabili da bisa ga cewarshi, zargin da ake yi mata na cin hanci da rashawa yana bata mashi suna.

Admiral Alison Madueke ya bayyana cewa, tsohuwar Ministar ta shigar da kara a wata kotun kolin jihar Nassarawa a shekarar 2021, ta nemi kotu ta kashe aurensu, kuma bai kalubalanci neman kashe auren ba sabili da haka, a ranar 13 ga watan Afrilu, shekara ta 2022, kotu ta kashe auren. Sai dai yace, duk da yake an kashe auren, tsohuwar Minstar ta ci gaba da amfani da sunan shi.

Bisa ga cewar shi, Diezani ta fara amfani da sunan shi ne lokacin da aka ba ta mukamin Minista a zamanin mulkin Goodluck Jonathan daga shekara 2010 zuwa 2015.

Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani
Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani

Ya kuma bayyana ta bakin lauyoyin shi cewa, sun daina zama a matsayin miji da mata tun shekarar 2015 lokacin da ta bar mukaminta na Minista ta kaura zuwa Ingila. Ya ce, tun daga wannan lokacin suke zaman kansu.

Rear Admiran Madueke da Diezani sun yi aure ranar 30 ga watan Yuni shekarar 1999, suna kuma da ddaya tsakaninsu.

Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani
Tsohuwar Minsitar kudin Najeriya Diezani

Yace duk da yake lauyoyinta sun rubuta mata wasika tun ranar 14 ga watan Disamba bara da bayyana bukatar ta daina amfani da sunan shi, ta koma amfani da sunan mahaifinta, amma ta ci gaba da amfani da sunan na shi, ta kuma ki bada amsar wasikar.

Banda daina amfani da sunan shi, Rear Admiran Madueke ya kuma bukaci Diezani ta wallafa a jaridun Najeriya da na Ingila cewa ta daina amfani da sunanshi, ta koma amfani da sunan mahaifinta Agama.

Banda Ministar albarkatun man fatir, Diezani Allison-Madueke kuma ta yi ministar tama da karaka tsakanin shekarar 2008 zuwa 2010, ta kuma yi ministar sufuri tsakanin shekarar 2007-2008.

An zabi Diezani Allison-Madueke a matsayin shugabar kungiyar kasashe masu arzikin man fetir (OPEC) mace ta farko a taron kungiyar na 166 da aka gudanar a Vienna ranar 20 ga watan Nuwamba, shekara ta 2024.

Tsohuwar Ministar ta bayyana lokacin da take matsayin Minista cewa, tana fama da sankaran mama kuma ana yi mata jinya a Ingila.

A shearar da ta gabata, hukumoni a kasar Ingila su ka tuhumi tsohuwar Ministar da laifin bada toshiya. Bayan ta bayyana a kotu a watan Oktoba aka bada belinta aka kuma sa ranar da za a ci gaba da sauraron karar.

A watan Oktoba shekara ta 2023, babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya kuma Ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya gabatar da wasikar sammacin kamo Diezani Alison-Madueke da kuma neman a tasa keyarta zuwa Najeriya ga kotun hukumar hukunta manyan laifuka ta kasar Birtaniya.

Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta na zargin tsphuwar Ministar da yin da rubda ciki da fadi Biliyoyin Naira, zargin da ta musanta, ta kuma ki bayyana gaban hukumomin Najeriya domin kare kanta.

nigeria-ex-oil--minister-charged-with-money-laundering

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG