Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamiti Ya Bada Shawarar Bincikar El-Rufa’i Akan Cin Amanar Mukami Da Halasta Kudaden Haram


Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Da yake gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar laraba, Shugaban Kwamitin, Henry Zacharia, yace ba’a yi amfani da galibin basussukan da gwamnatin El-Rufa’i ta ranto akan bukatun da suka sa aka karbosu ba, a yayin da wasu lokotanma, ba abi ka’idojin karbo bashin ba.

Kwamitin wucin gadin da Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta kafa domin bincikar badakalar kudade da basussuka da kwangilolin da aka bayar karkashin gwamna, Nasir El-Rufa’i ya gabatar da rahotansa ga majalisar.

Da yake gabatar da rahoton yayin zaman majalisar na ranar laraba, Shugaban Kwamitin, Henry Zacharia, yace ba’a yi amfani da galibin basussukan da gwamnatin El-Rufa’i ta ranto akan bukatun da suka sa aka karbosu ba, a yayin da wasu lokutanma, ba abi ka’idojin karbo bashin ba.

Don haka, kwamitin, ya bada shawarar hukumomin tsaro dana yaki da cin hanci da rashawa su gudanarda bincike tare da gurfanar da El-Rufa’i da mukarraban gwamnatinsa da aka samesu da laifin cin amanar mukami da saba ka’idojin bada kwangila da karkatar da kudaden al’umma da halasta kudaden haram da suka jefar jihar Kaduna cikin kangin basussuka.

Har ila yau kwamitin ya bada shawarar dakatar da Kwamishinan Kudin jihar Kaduna, Shizer Badda, nan take, wacce ta taba rike mukamin a lokacin gwamnatin El-Rufa’i, tare shugaban Hukumar Ilmin Bai Daya na jihar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG