Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lauyan Trump Na Kokarin Hana Wallafa Wani Littafi Kan Shugaban Na Amurka


Trump (hagu) tare da Steve Bannon (dama) a lokacin yakin neman zabe
Trump (hagu) tare da Steve Bannon (dama) a lokacin yakin neman zabe

Wani lauyan shugaba Donald Trump na Amurka yana kokari a yau alhamis ya hana wallafa wani littafin da ake shirin yi a mako mai zuwa, inda aka yi bayanin abubuwan da suka wakana a shekarar farko cikin fadar White House. Lauyan yace littafin na bata suna da kuma kage ne.

Lauya Charles Harder ya rubuta ma marubucin littafin, Michael Wolff, da kamfanin wallafa littattafai na Henry Holt and Co., wasika yana neman da a dakatar da wallafa wannan littafi mai suna "Fire and Fury: Inside the Trump White House" wadda aka shirya za a yi a ranar talata. Lauya Harder yace suna "binciken wasu bayanai na kage ko marasa tushe" da aka fadi kan Trump a cikin wannan littafi, bayanan da marubuci Wolff yace ya samo daga hirarraki fiye da 200 da ya gudanar da mutane a lokacin yakin neman zaben Trump da kuma bayan da aka rantsar da shi ya kama aiki shekara guda da ta shige.

Wasu bayanan da aka gutsuro daga cikin littafin jiya laraba, sun janyo mummunar cacar baki a nan Washington jiya laraba. 'Yan sa'o'i kadan bayan samun wadannan bayanan, Harder ya aike da wasikar jan kunne, tare da neman rufe bakin tsohon babban jami'in tsare-tsaren na shugaba Trump, Steve Bannon, wanda aka ambata sau da dama cikin littafin, inda lauyan ya bukaci da ya daina yin kalamun bata sunan Trump da iyalansa,

Kakakin fadar White House, Sarah Sanders, ta ce shugaba Trump yayi tsananin fusata da kalamun Mr. Bannon.

A cikin furuci mafi zafi, an ambaci Bannon yana fadin cewa a wurinsa, "cin amanar kasa" ne kuma "rashin kishi" ganawar da babban dan shugaba Trump, Donald Trump Junior, da surukin shugaban Jared Kushner da kuma manajan yakin neman zaben shugaban na wancan lokaci Paul Manafort, suka yi da wasu 'yan kasar Rasha a tsakiyar lokacin yakin neman zabe kuma a cikin gidan shugaban na Trump Tower dake New York. Wani wakilin 'yan Rasha din ya fadawa dan shugaba Trump a lokacin cewa zasu mika masa wasu bayanan sirrin da zasu bata sunan abokiyar hamayyar Trump, Hillary Clinton 'yar takarar jam'iyyar Democrat, a wani bangare na kokarin da gwamnatin Rasha take yi domin taimakawa Trump ya lashe zabe. Daga baya Trump karami yace babu wata shaidar da aka ba shi a wannan ganawar.

'Yan sa'o'i kadan bayan da aka fara wallafa wasu bayanai daga cikin littafin, shugaba Trump ya hau kan shafinsa na Twitter yana cewa, "Steve Bannon bai taka wata rawa a wuri na ko shugabanci na ba. A lokacin da na kore shi, ba ma aikinsa kawai ya rasa ba, har ma hankalinsa ya tabu."

Trump yace Bannon ya shiga harkar siyasar shugaban ne don daukaka kansa kawai, ya kuma "shafe tsawon lokacin da yayi a fadar White House yana fallasa bayanai na karya ga 'yan jarida domin ya nuna kamar cewa shi wani jigo ne fiye da mukaminsa."

Duk da wannan caccaka da shugaba Trump yayi masa, Steve Bannon ya fito daren jiya laraba yana bayyana shugaban a zaman wani gagarumin jigo, tare da cewa "babu wani abinda zai shiga tsakaninmu da shugaba Trump da kuma ajandarsa."

A yau alhamis, shugaba Trump yace, "ai kun ji jiya da daddare ya ce ni gagarumin jigo ne. Da alamu ya sauya salon rawarsa cikin gaggawa."

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG