Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Da Tsohon Hadiminsa Su Na Kazamin Rikici


Shugaba Trump da Mista Steve Bannon
Shugaba Trump da Mista Steve Bannon

Wani sabon littafi ya janyo sanya kafar wando guda tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da wani tsohon babban hadiminsa Steve Bannon, al'amarin da ya zo da jama'a da bazata. Tuni masu sharhi kan al'amura ke cewa wannan rigimar za ta raba ma Shugaban hankali kuma tasirinta zai zarce Amurka.

A wani al’amari mai ban mamaki, Shugaban Amurka Donald Trump da tsohon babban hadiminsa Steve Bannon sun shiga wani rikici mai tsanani, bayan da wani sabon littafin da ke dab da fitowa ya ruwaito Mista Bannon na cewa wani dan Shugaba Trump ya ci amanar kasa saboda ganawa da wasu jami’an kasar Rasha da ya yi. Bannon ya ce da wuya ace Trump bai da masaniya game da wannan ganawar.

Littafin ya kuma ruwaito Mista Bannon na cewa diyar Trump, Ivanka Kushner, sakara ce kawai hulokuwa. Wannan ya sa ba tare da bata lokaci ba Shugaba Trump ya mai da martani ta wajen caccakar Mista Bannon ya ce ikirarin Bannon cewa ya yi matukar tasiri wajen nasarar da Trump ya yi a zabe maganar banza ce kawai. Trump y ace shi daga yanzu ma babu ruwansa da Mista Bannon.

Kan wannan takaddamar na tuntubi wani mai fashin baki kan al’amauran Amurka da ke zaune a nan Amurka mai suna Hassan Lawal Sallau Jibiya don ya yi fashin bakin al’amarin, sai ya ce lashakka wannan rigimar za ta janyo matsaloli a ciki da wajen Najeriya. Ya ce zargin da Mista Bannon ya yi zai kuma nuna sahihancin binciken da ake yi game da zargin hadin baki tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump da kasar Rasha.

Ga cikakkiyar hirar, inda aka fara tambayar Hassan abin da zai fara cewa game da wannan rigimar sai ya ce:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG