Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi Ya Mutu


ITALY-BERLUSCONI
ITALY-BERLUSCONI

Tsohon Firaministan Italiya wanda aka yi ta takaddama da shi, Silvio Berlusconi, ya mutu yana da shekaru 86 da haihuwa a duniya.

Hamshakin attajirin mai kafofin yada labarai ya mutu ne sakamkon cutar sankaran jini.

Berlusconi ya fara samun dukiyarsa ne daga harkar gina gidaje sannan ya ci gaba zuwa kafa gidan talabijin wanda ya yi nasara sosai a kai. A wani lokaci, an san shi a matsayin mutumin da ya fi kowa arziki a Italiya.

Sannan ya tsunduma cikin harkokin siyasa, fagen da masana suka ce ya Amurkantar.

Shi dai wannan dan siyasar mai ra’ayin rikau ya yi aiki a matsayin Firai minista a gwamnatoci hudu tun daga shekarar 1994. Berlusconi ya fuskanci tarin badakaloli na siyasa a lokaci fafutukarsa ta siyasa.

An san shi da son bukukuwa masu nasaba da badala da karuwai, kuma a wani lokaci ma ya fuskanci tuhumar biyan kudi ga wata matashiya mai rawa da ciki don yin lalata da ita. Amma daga bisani an wanke shi daga wadannan tuhume tuhumen.

Wadannan badakaloli ba su hana shi barin tarihi na gina siyasa mai dorewa ba. “Shi ne mutumin da ya hada kan masu ra’ayin rikau na Italiya,” in ji Roberto D’Alimonte, farfesa a fannin siyasa a jami’ar Luiss da ke Rome a hirarsa da jaridar Financial Times. Ya kara da cewa, “Ya sanya su ka karbu kuma ake gogawa da su.”

XS
SM
MD
LG