Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mijin Sauraniyar Ingila Yarima Philip Ya Mutu


Prince Philip
Prince Philip

Yarima Philip, wanda ya auri Sarauniya Elizabeth a shekarar 1947, ya rasu ne a ranar Juma'a, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Rueters ya ruwaito.

Rahotanni daga Masarautar Burtaniya na cewa mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya rasu. Shekararsa 99.

“Cikin yanayi na alhini, Sarauniyar Ingila, na sanar da mutuwar mijinta, Mai Martaba Yerima Philip, Duke na Edinburg,” Sanarwar da fadar ta fitar ta ce.

Marigayi Philip ya rike sarautar Duke of Edinburgh, ya kuma kasance ginshiki ga Sarauniyar Ingila, wacce al’amuranta ke da ban mamaki.

Ya fara haduwa da Sarauniya Elizabeth ne a lokacin yana samun horon zama sojan ruwa. Ta kasance gimbiya mai kunya. Sun kuma yi aure a shekarar alif dari tara da arba’in da bakwai.

Bayan da ta zama sarauniya, Yarima Philip ya shiga tsaka-mai wuya kan barin aikinsa na sojan ruwa, a cewar Philip Eade, wanda ya rubuta littafin “Young Prince Philip” – wato matashi yarima Philip.

“Ya kasance mutum da ya samu daukaka, wanda ake girmamawa a rundunar sojin ruwan Burtaniya, kuma har ya dauki hanyar zama shugaban rundunar sojin ruwan kasar, a ce mutum duk ya yi watsi da wannan daukaka ya koma ya zama mai marawa matarsa baya. Mutum ne mai kwarjini.” Eade ya ce.

A lokacin wata hira da aka yi da shi, an tambayi Yarima Philip, kan yadda yake tunanin matsayinsa a masarautar, sai ya kada baki ya “ba na ma tunanin hakan.”

“Yarima Philip ya girma da tunanin cewa babbar rawar da zai taka ita ce taimakawa sarauniya Elizabeth a aikinta, kuma babu haufi, ya karbi wannan matsayi hannun bi-biyu, ya kuma zama mai abin da ya fi dauka da muhimmanci. In ji marubuci Philip Eade.

Sama da shekara 70, Yarima Philip, ya fuskanci rayuwa mai dadi da akasin haka, a matsayinsa na daya cikin iyalan masarautar Burtaniya, ciki har da mutuwar Gimbiya Diana a shekarar 1997.

Yarima Philip, mutum ne da aka san shi da barkwanci, wani makami da ya yi amfani da shi wajen kore masu ikrarin cewa shi yana zaman mataimaki ne kawai.

A lokacin wani jawabi da ya yi a shekarar 1956, yayin bude gasar wasannin Olympics, Yarima Philip ya taba cewa, “na kaddamar da bude gasar wasannin Olympics na Melbourne.”

A wasu lokuta, barkwancinsa kan batawa wasu rai.

Amma duk da haka, ya taka muhimmiyar rawa a masarautar, wacce ya taimakawa wajen samar da sauye-sauye.

Gimbiya Diana
Gimbiya Diana

“Wannan wani abu ne da Philip ya yi ta hange a kai, inda ya rika muradin ganin an samar da sauye-sauye a masarautar. Misali, a lokacin bikin nadin sarautar da aka yi wa Sarauniya Elizabeth ta biyu a shekarar 1953, ya goyi bayan a nadi taron da na’urar daukan hoto ta talbijin. Wasu za su yi tunanin shi mutum ne dan gargajiya mai ra’ayin mazan jiya, amma ba haka lamarin yake ba. Yarima Philip ya kalli fasahar talbijin a matsayin abin da duniya za ta karba anan gaba, saboda mutane suna bukatar su rika ganin masu mulkarsu.” In ji Matthew Glencross, masanin tarihi a Kings College da ke London.

A shekarar 2017 Yarima Philip ya yi ritaya daga ayyukan masarautar

Bayan shekara daya, ya gamu da wani mummunan hadarin mota a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa gidan iyalan masarautar ta Ingila da ke Sandringham.

Lokaci na karshe da aka gansa a baina jama’a, shi ne a watan Yulin shekarar 2020 a fadar masarautar ta Windsor Castle.

Aiwatar da aikinsa na zama miji da kuma uba, Yarima Philip ya taka muhimmiyar rawa a wannan masarauta mai shekara dubu daya da dari biyu, daga inda ya kan tsaya taku biyu a bayan Sarauniya Elizabeth.

Takaitaccen Tarihin Yarima Philip Wanda Ya Mutu A Ranar Juma'a 9 Ga Watan Afrilu 2021
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG