Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Dan Majalisar Dattawan Amurka, Joe Lieberman Ya Mutu


Joe Lieberman
Joe Lieberman

Tsohon sanatan Amurka kuma wanda jam’iyyar Democrats ta amince ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa karkashinta, Joe Liebeman, ya riga mu gidan gaskiya yana mai shekaru 82 a duniya bayan da ya sha fama da wani rauni sakamakon wata faduwa da ya yi, kamar yadda danginsa su ka fada jiya Laraba.

Mai dakin shi Hadassah da sauran dangin shi suna tare da shi a sa’adda rai yayi halinsa, abin da aka sanar cikin sanarwar kenan.

Sanata Lieberman ya kasance mai kaunar Allah, iyalen shi da kuma Amurka; ya jajirce iya tsawon rayuwar shi wajen taimakawa al’umma”.

Lieberman shi ne wanda jam’iyyar Democrats ta amince a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben da jam’iyyar Republican George W. Bush ya ci.

A shekara ta 2004 ne Lieberman ya nemi takarar shugaban kasa a jam'iyyar Democrat, amma goyon bayansa ga yakin Iraki ya kawo karshen takararsa a wajen masu jefa kuri'a, a daidai lokacin da ake kara nuna fushi kan mamayar da kuma zubar da jini da ya biyo bayan yakin. Don haka 'yan Democrats na Connecticut suka ƙi Lieberman lokacin da ya tsaya takarar neman wa'adin majalisar dattijai na huɗu a jihar a 2006.

Lieberman ya bayyana goyon bayansa da murya mai karfi ga 'yancin 'yan luwadi, 'yancin jama'a, 'yancin zubar da ciki da kuma abubuwan da suka shafi muhalli wanda sau da yawa ya sha yabo daga yawancin 'yan Democrat. Ya kuma taka muhimmiyar rawa a cikin dokokin da suka kafa Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG