Karawar kasashen biyu wani lamari ne da ke cike da tarihi, inda aka kwatanta haduwarsu shekaru 24 da suka gabata a Legas.
Nasarar da Afirka ta Kudu ta samu a wasan AFCON inda yazo ba zato ba tsammani ya dauki hankulan mutane, musamman yadda suke nuna bajinta a bugun fanareti.
Manazarta dai sun yabawa yadda Afirka ta Kudu ta yi taka-tsan-tsan da shirye-shirye da nazari kan dabaru, wadanda suka taimaka wajen samun nasarar da suka samu ya zuwa yanzu.
Sabanin haka, manazarta kwallo da dama sun nuna damuwar su kan tsarin tsaron Najeriya da kuma tunanin rashin kai hare-hare da dama.
Manazarta sun jaddada bukatar samar da dabarun da za su yi amfani da damar cin kwallaye, ta yadda za a kaucewa dogaro da bugun fanareti.
jiga-jigan jarumai irin su Oliseh da Babangida a wata hira da sukayi da gidan talabijin na cikin gida (channels) sunyi kokarin zaburarwa ‘ga 'yan wasan na yanzu.
Oliseh da Babangida, na daga cikin jiga-jigan ‘yan wasan Najeriya da suka samar ma kasar da nasarori a a baya, sun nuna kwarin gwiwa kan yadda Super Eagles za ta iya doke Afrika ta Kudu.
An shirya fafatawar da ba za a manta da ita ba, inda kungiyoyin biyu ke shirin barin tabo maras gogewa a gasar. Yayin da ake ta jira, manazarta harkar kwallon kafa na cigaba da nazarin yadda wasan kan kaya a ranar Laraban nan mai zuwa.
Najeriya da Afirka ta Kudu za su fafata a wasan kusa da karshe a ranar Laraba, 7 ga Fabrairun da mu ke ciki da misalin karfe 6 agogon Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna